1 Corinthians 16

Bayarwa saboda Mutanen Allah

1To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. 2A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yǎ keɓe ʼyan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yǎ ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. 3In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima. 4In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.

Roƙona

5Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku-domin zan ratsa ta Makidoniya. 6Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni. 7Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ʼyan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda. 8Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentikos, 9domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.

10In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11Kada fa wani yǎ ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yǎ koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ʼyanʼuwa.

12Batun ɗanʼuwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yǎ zo wurinku tare da ʼyanʼuwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.

13Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi. 14Ku yi kome da ƙauna.

15Kun san cewa iyalin gidan Istifanus ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ʼyanʼuwa, 16ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa. 17Na yi farin ciki da isowar Istifanus, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba. 18Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.

Gaisuwa ta Ƙarshe

19Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu. 20Dukan ʼyanʼuwa a nan suna gaisuwa. Ku gai da juna da sumba mai tsarki.

21Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.

22Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji-laʼana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji
Da Aramayik kalman nan Zo, Ya Ubangiji ita ce Maranata.
!

23Alherin Ubangiji Yesu yǎ kasance tare da ku.

24Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā ba su da Amin.


Copyright information for HauSRK